Gwamnatin Tarayyar Najeriya | |
---|---|
political system (en) | |
Bayanai | |
Ƙasa | Najeriya |
Shafin yanar gizo | nigeria.gov.ng |
Gwamnatin tarayyar Najeriya tana da rassa guda uku: Ƴan majalisar zartaswa, da shari'a waɗanda kundin tsarin mulkin Najeriya ta ba su iko da Majalisar shugaban kasa da kotunan tarayya ciki har da kotun koli. Kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadi rarraba muƙamai da daidaito a tsakanin bangarorin guda uku (3) da nufin hana maimaita kura-kuran da gwamnati ta yi a baya.[1][2]
Najeriya jamhuriya ce ta tarayya, wacce shugaban ƙasa ke da ikon zartarwa. Shugaban ƙasa shi ne shugaba a ƙasa, jagoran gwamnati, kuma shugaban tsarin jam’iyyu da yawa. Siyasar Najeriya tana gudana ne a cikin tsarin tarayya, shugabancin ƙasa, jamhuriya dimokuradiyya mai wakilci, inda gwamnati ke amfani da ikon zartarwa. Ƴan majalisa na ƙarƙashin gwamnatin tarayya da kuma majalisun dokoki guda biyu: Majalisar wakilai da kuma ta dattawa. A dunƙule, majalisun biyu su ne hukumar da ke kafa doka a Najeriya, wadda ake kira majalisar dokokin ƙasar, wadda ke zaman tantance bangaren zartarwa na gwamnati.[3] "Economist Intelligence Unit" ya kimanta Najeriya a matsayin "hybrid regime" " a shekara ta 2019.[4] Gwamnatin Tarayya, Jihohi, da Kananan Hukumomin Najeriya na da burin yin aiki tare domin gudanar da mulkin kasa da al’ummarta.[5] Najeriya ta zama mamba ja kungiyar Commonwealth ta Burtaniya bayan samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka a ranar 1 ga watan Oktoba, shekara ta 1960.[6]